
Kungiyar dattawan Yarbawa ta Afenifere ta yi kira ga shugaba kasa, Bola Ahmad Tinubu da ya gaggauta amincewa da kafa ‘yansandan jihohi.
Kungiyar ta bayyana hakane bayan taro na masu ruwa da tsaki da ta yi a gidan shugabanta, Chief Reuben Fasoranti dake Akure.
Ta yi kira ga shugaban kasar da ya fitar da kudirin doka wanda zai bayar da damar canja kundin tsarin mulkin Najeriya dan a samar da ‘yansandan Jihohi inda tace ya aika da wannan kudirin dokar zuwa majalisa.
Hakan na kunshene a cikin sanarwar da sakataren yada labaran Kungiyar, Jare Ajayiya fitar inda yace sun yaba da kokarin Gwamnati na magance matsalar tsaro amma akwai bukatar a kara himma.