
Kungiyar Kwadago ta NLC ta yi barazanar shiga yajin aiki muddin gwamnati bata mutunta alkawarin da suma cimmawa ba.
Kungiyar ta bayyana cewa sun cimma matsayar cewa za’a rage karin kudin kiran waya dana data da aka yi da kaso 50 zuwa 35.
Kungiyar tace idan Gwamnatin ta kasa mutunta wannan yarjejeniyar sun sanar da wakilansu na fadin Najeriya cewa su shirya yin zanga-zanga.