Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya ta ce amincewa da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza da kwamitin sulhu na MDDr ya yi, wani mataki ne na goyon bayan samar da zaman lafiya.
Linda Thomas-Greenfield ta ce ƙasashen duniya sun haɗa kai kan yarjejeniyar da za ta ceci rayuka, da mayar da mutanen Isra’ila da aka yi garkuwa da su gida da kuma taimaka wa fararen hula Falasdinawa.
A rubuce dai ƙudurin na nuna cewa Isra’ila ta amince da yarjejeniyar wadda shugaba Biden ya sanar a watan jiya.
Ita ma Hamas ta yi maraba da ƙuri’ar da Majalisar ta kada, amma har yanzu ba ta mayar da martani a hukumance ba.
Wakiliyar BBC ta ce Amurka ta ce za ta ba da tabbacin cewa Isra’ila zata yi biyayya ga yarjejeniyar, muddin Hamas ta amince da ita.
A yau Talata ne sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken, zai halarci wani taron bayar da agaji ga al’ummar Gaza da za a yi a Jordan.