Friday, December 5
Shadow

Kwana daya bayan samun Rahoton cewa, zai fito takarar shugaban kasa, Gwamnatin Tarayya ta fara sukar Tsohon Shugaban kasa, Goodluck Jonathan

Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana cewa tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan na da ‘yancin tsayawa takarar shugabancin ƙasar a shekarar 2027.

Sai dai ta jaddada cewa ‘yan Najeriya ne za su yi masa hukunci saboda ba su manta ‘munin’ mulkin Jonathan ba, ta kuma kwatanta mulkin Tinubu da abin da ta bayyana a matsayin “gagarumin ci gaban tattalin arziƙi”

Fadar shugaban ƙasar ta kuma ɗora alhakin fara yaƙin neman zaɓe da wuri kan masu neman kifar da shugaba mai ci.

Hakan na zuwa ne a rana guda da jam’iyyar PDP ta bayyana cewa ba za ta bai wa Jonathan tikitin tsayawa takara kai tsaye ba, inda ta bayyana shi a matsayin ɗaya daga cikin “zaɓuɓɓukan da take dubawa.

Karanta Wannan  Ku kara hakuri dani, ku bani Lokaci>>Shugaba Tinubu ya roki 'yan Najeriya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *