Tsohon gwamman jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya saka mutane rudani bayan da aka ganshi a hedikwatar Jam’iyyar SDP a ranar Talata.
Hakan na zuwane kwanki biyu bayan da Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya karyata labaran da suka ce ya bar Jam’iyyar APC zuwa PDP.
Tsohon shugaban NIMASA, Ahmad Tijjani Ramalan ne ya wallafa hotunan zuwan El-Rufai ofishin SDP.
Ya bayyana cewa an yi zama tsakanin El-Rufai da SDP ne a kokarin da ake na yin hadaka dan samo hanyar yin nasara akan Jam’iyyar APC a zaben shekarar 2027.