Wednesday, July 29
Shadow

Kwankwaso dansa, Mustapha ya so tsayarwa takarar Gwamnan Kano a jam’iyyar NDC>>Jigo a jam’iyyar NDC ya fasa Kwai

Rufai Hanga na jam’iyyar NDC ya fasa Kwai cewa, Kwankwaso dansa, Mustapha yaso tsayarwa takarar gwamnan jihar Kano a jam’iyyar.

Ya bayyana hakane a wata hira da aka yi dashi a wani gidan radiyon Kano, kamar yanda jaridar Daily post ta ruwaito.

Hanga yace Kwankwaso ya aika masa da tawaga bisa jagorancin shugaban jam’iyyar NDC a jihar Kano, Hussaini Isa Mairiga inda ya shaida masa cewa, yana son tsayar da dansa, Mustapha a matsayin dan takarar Gwamna a jam’iyyar NDC.

Hanga yace ya musu fatan Alheri kuma yace a gayawa Kwankwaso a shirye yake ya zama manajan yakin neman zaben Dan Kwankwason.

Yace bai kara ji daga wajansu ba, sai daga baya Aminu Abdussalam ya sameshi yace masa Kwankwaso ya bashi takarar Gwamna kuma yana son ya zama mataimakinsa.

Karanta Wannan  Daga ƙarshe dai an buɗe wa Jarumar Tik-Tok Rahama Sa'idu sabon shago kyauta a garin Zaria, bayan barin Kano da tayi

Hanga yace duk da yasan cewa mukamin mataimakin Gwamna a wajansa kaskanci ne amma ya amince.

Yace kuma bayan kwana biyu sai ji yayi Kwankwaso ya baiwa dansa, Mustapha mukamin takarar na mataimakin gwamna.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *