Wednesday, July 29
Shadow

Wata Sabuwa: Ina nan a jam’iyyar NDC bani da shirin komawa APC>>Inji Rufai Hanga

A yayin da dukkan alamu suka nuna cewa Sanata Rufai Hanga ya kammala shiri tsaf dan komawa jam’iyyar APC, har ma aka ga wasu rahotanni na cewa ya ma riga ya koma APC.

A yanzu ya fito yace bashi da shirin barin jam’iyyar NDC ya koma APC.

Sanata Rufai Hanga ya bayyana hakane a wata hira da aka yi dashi a wani gidan Rediyo na Kano.

Hakan na zuwane bayan da aka ganshi ya gana da jiga-jigan jam’iyyar APC ciki hadda shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.

Rufai Hanga yace Jam’iyyar su ta NDC ba zata ci zaben shugaban kasa ba amma zata ci Kano.

Karanta Wannan  Mai Martaba Sarkin Daura Ya Tunbuke Rawanin Wani Dagaci Bayan Kama Shi Da Laifin Yin Ĺàlàțà Da Wata Maťar Àurè Bayan Ya Yi Garkuwà Da ità

Da yake magana kan alakarsa da Kwankwaso yace tana nan kuma har yanzu suna girmama juna.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *