Friday, December 26
Shadow

Labarin cewa mun dakatar da El-Rufai tsayon shekaru 30 karyane, Munafurcin jam’iyyar APC ne>>Inji Jam’iyyar SDP

Jam’iyyar SDP me doki inda tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya koma ta karyata labarin da yayi yawo sosai cewa, ta dakatar da El-Rufai tsawon shekaru 30.

Kakakin jam’iyyar a jihar Kaduna, Hon. Darius Kurah ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai inda ya bukaci mutane su yi watsi da wanan magana.

Yace wanda aka ce ya fitar da labarin me suna, Araba Rufus Aiyenigba wanda aka ce kakakin jam’iyyar SDP ne karyane bashine kakakin jam’iyyar SDP na kasa ba.

Yace kuma abinda ake yadawa cewa, wai El-Rufai na munafurtar jam’iyyar SDP shima ba gaskiya bane.

Karanta Wannan  Kalli Hotuna da Duminsu: Har an canja sunan Jami'ar UNIMAID dake Maiduguri zuwa Muhammadu Buhari University

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *