Majalisar wakilai ta gayyaci ministoci 3 da suka hada da na Noma, da samar da abinci, Abubakar Kyari da na kimiyya da fasaha da kirkire-kirkire, Uche Nnaji, dana kasafin kudi da tsare-tsare, Atiku Bagudu dan su mata bayani kan yanda aka kashe Dala Biliyan $2 da aka bayar dan samarwa da Najeriya wutar lantarki.
Kwamitin kula da makamashi na zamani na majalisar ne suka gayyaci ministocin.
Kudin an samo su ne daga tallafi da kuma zuba jari dan samarwa da Najeriya wata hanya ta daban ta samun wutar lantarki banda wadda ake da ita.
Kuma an samu kudinne daga shekarar 2015 zuwa yanzu.
A ranar Talata da Larabane dai ministocin zasu gurfanar gaban majalisar dan bayar da ba’asi kan yanda aka kashe wadannan kudade.
Majalisar ta nuna damuwa kan cewa duk da wadannan kudade amma gashi wutar lantarki ta ki ingantuwa a kasarnan.
Saidai a zaman kwamitin na ranar Talata, babu ko minista daya daya halarci zaman inda duk suka aika wakilai, saidai duka majalisar ta mayar dasu inda tace ba zata sauraresu ba inda aka bukaci sai ministocin da kansu sun halarci zaman.
Shugaban kwamitin, Afam Ogene ya bayyana cewa suna son ganin duka ministocin da aka gayyata ba tare da wani uzuri ba ranar Laraba.