
Wani Lauya ya bayyana yanda mutane zasu iya mallakar Gida Kyauta ba tare da ko sisi ba.
Ya bayyana cewa mutum kawai duk gudan da ya ba kowa ya shiga ya zauna.
Yace idan mutum ya kai shekaru 10 zuwa 12 a cikin gidan kuma me gida bai zo ba, to gidan ya zama nashi, yace amma idan me gidan yazo kamin shekaru 10 zuwa 12 za’a kwace ne a bashi kayanshi.
Yace amma idan ya wuce wadancan shekarun bai zo ba, to gidan ya zama mallakin wanda ke zaune a ciki kuma ko kotu aka je ba za’a kwace gidan ba.