Thursday, August 20
Shadow

Likitan Tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya tabbatarwa da ICPC cewa shine ya bayar da takardar da ake zargin ta bogi ce dan a bayar da belin El-Rufai

Likitan tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai, Abubakar Muhammad ya gayawa ICPC cewa shine ya bayar da takardar lafiya da ake takaddama akanta.

Likitan yace shine ya ya bayar da takardar amma bayanan dake kan takardar bana bogi bane.

ICPC ta yi zargin cewa bayanan dake kan takardar lafiyan na bogi ne kuma an yi hakanne dan a samu bayar da belin malam Nasiru Ahmad El-Rufai.

Saidai Likitan yace bayanan dake kan Takardar na gaskiya ne bai saba dokar aikinsa wajan bayar da takardar ba.

Yace kuma sun dade tare da malam Nasiru Ahmad El-Rufai tun shekarar 2005, yace ta hannnun matarsa suka san juna.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Duk wata Jarumar fim a Yanzu ya kamata na zamar mata Darasi, In kina jin Daukaka ne, na samu abinda kika samu amma yau komai ya kare>>Ummi Nuhu a sabuwar hira

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *