Monday, April 6
Shadow

Likitocin Kano sun dakatar da shiga yajin aiki

A jihar Kano, ƙungiyar likitoci ta umarci likitocin jihar su koma bakin aiki bayan janye yajin aikin da aka wayi gari da shi a asibitin ƙwararru na Murtala Muhammad a ranar Alhamis.

Likitocin dai sun shiga yajin aikin ne bayan cikar wa’adin sa’o’i 48 da ƙungiyar ta baiwa gwamnan jihar, na ya kori kwamishiniyar jin ƙai ta jihar, Amina Abdullahi HOD, bisa zargin cin zarafin wata likita a asibitin, zargin da ta ce musanta. Duk da cewa likitocin sun janye yajin aikin amma ƴan sa’o’in da aka shafe babu likitoci a asibitin na Murtala Muhammad har an ga tasirinsa, inda ya shafa majinyata.

Karanta Wannan  Dan gidan tsohon Gwamnan Kaduna, Bello El-Rufai ya fallasa abinda ICPC kewa mahaifinsa na rashin kyautawa yayin da suke tsare dashi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *