Wata mata me zaman kanta a jihar Adama ta kashe me sayar da giya bayan da rikici ya barke a tsakaninsu akan canjin Naira 200.
Matar me suna Riyanatu Musa ta kashe Yohanna Musa ne ta hanyar caka masa wuka a kirji.
Hukumar ‘yansandan jihar ta tabbatar da faruwar lamarin inda tace wadda ake zargi ta amsa laifin da ake zarginta dashi.
Tace a lokacin data kashe Yohanna Musa bata cikin maye inda tace amma ta yi nadamar abinda ta aikata.
Kakakin ‘yansandan jihar, SP Suleiman Nguroje yace kwamishinan ‘yansandan jihar, Morris Dankombo ya bayar da umarnin yin bincike kan lamarin.