
Shahararren me kudin Duniya, Bill Gates ya bayyana cewa, mafi yawancin kudinsa da suka kai dala Biliyan $200 a Africa zai rabar dasu.
Bill Gates ya bayyana hakanne a wajan taron kungiyar hadin kan kasashen Africa da ya gudana a Addis Ababa, Ethiopia.
Yace mafi yawancin kudin zai bayar dasu ne karkashin kungiyarsa ta Gates Foundation kuma za’a yi amfani dasu ne wajan inganta harkar Lafiya da Ilimi.