
Hukumar kula da sararin samaniyar Najeriyar, The Nigerian Meteorological Agency ta bayyana cewa, za’a yi ruwan sama aosai a jihohi daban-daban na Najeriya daga ranar Lahadi zuwa Litinin.
Tace ruwan zai sauka a jihohin Taraba, Kebbi, Zamfara, Kaduna, da Adamawa ranar Asarar.
Da kuma jihohin Kebbi, Taraba, Zamfara, Borno, Kaduna, Sokoto, Gombe, Bauchi.
Imo, Enugu, Abia, Ebonyi, Anambra, Ondo, Oyo, Ogun, Ekiti, Edo, Lagos, Cross River, Akwa Ibom, Delta, Bayelsa, da Rivers.
Hukumar ta kuma yi hasashen za’a sake yin ruwan ranar Litinin a Arewa da kudu.