Maganar gaskiya Tinubu na ƙoƙari wajen gyaran tattalin arzikin ƙasa kuma ya cancanci a ƙarfafi Gwiwarsa – Fayose.

Ayodele Fayose, tsohon gwamnan jihar Ekiti, ya ce ziyararsa ga Shugaba Bola Tinubu ta kasance ta kashin kai ne domin ƙarfafa masa gwiwa.
“Ziyarata na kashin kai ce, domin ƙara ƙarfafa shi ya cigaba da abin da yake yi domin ‘yan Najeriya. Babu wanda ya ce abu ne mai sauƙi, amma babu wani mu’ujiza da zai iya sauya lamura cikin dare ɗaya,” in ji Fayose ga manema labarai a Legas ranar Litinin bayan ganawarsa da shugaban ƙasa.
Ya ce Tinubu ya cancanci yabo bisa ƙoƙarinsa har zuwa yanzu.
“Amma saboda abinda shugaban ƙasa ya riga ya yi, dole ne mu yaba masa,” in ji shi.
Tsohon gwamnan ya ce tarihin sukar da ya yi wa gwamnatoci baya bai hana shi gane irin ƙoƙarin Tinubu ba.
“Ni na kasance mai sukar gwamnatin da ta gabata, amma ba za ka iya kwatanta halin da ake ciki yanzu da na baya ba,” in ji shi.
“Saboda haka, na zo ne da farko domin amfani da damar dawowarsa gida, in gan shi kuma in ƙarfafa shi ya ƙara yi wa ‘yan Najeriya aiki.”
Fayose ya ce tun yana gwamna karkashin jam’iyyar PDP, ya riga ya gaskata da irin shugabancin Tinubu.