Bugawar zuciya da sauri na iya faruwa a kowane lokaci kuma abune wanda ke zuwa ya wuce, akwai hanyoyi da yawa da ake amfani dasu wajan Maganin bugawar zuciya da sauri.
Ga abubuwan dake kawo bugawar zuciya da sauri kamar haka:
Motsa jiki.
Kishirwa me tsanani.
Rashin Lafiya.
Shiga halin takura.
Me ciki na iya fuskantar hakan.
Shaye-shayen miyagun kwayoyi.
Shan taba
Wasu daga cikin maganin bugawar zuciya da sauri sune:
Tashin Hankali:Tayar da hankali na sa bugawar zuciya da sauri, dan haka neman maganin kwanciyar hankali da samun nustuwa zai taimaka magance wannan matsalar.
Hanya ta gaba wajan magance matsalar bugawar zuciya da sauri itace a kwanta a kan gadon baya ko kuma ace rigingine sai a rika yin kamar ana tari, a dan rike numfashi sai a sakeshi.
Ana kuma iya yin wanka da ruwan sanyi.
Ana iya watsa ruwan sanyi a fuska.
Ana iya samun tsumma a saka kankara a cikinsa a nade a dora a fuska na tsawon akalla dakika 30.
Shan Ruwa: Idan kishi ya maka yawa, yakan sa jinin jikinka yayi kauri ta yanda zuciyarka zata rika aiki fiye da yanda ya kamata wajan harbashi. Dan hakane ake son idan kaji bugun zuciya da sauri to ka sha ruwa sosai.
Cin Ayaba da dankalin Hausa yana taimakawa sosai wajan magance matsalar bugawar zuciya da sauri.
Abubuwan da ya kamata a kiyaye sune:
Shan taba
Shan wiwi.
Shan Giya.
Magungunan tari dana mura masu cutarwa.
Maganin ciwon Hauka.
Maganin Hawan Jini.
Shan Hodar Iblis da sauransu.