Wednesday, January 15
Shadow

Maganin ciwon mara bayan saduwa

Akwai magunguna da yawa da ake amfani dasu Dan magance matsalar ciwon Mara bayan saduwa, wasu na asibiti ne, wasu kuma na gargajiyane da za’a iya yi a gida.

A wannan rubutun, zamu bayyana muku duka magungunan ciwon Mara bayan saduwa na asibiti Dana gargajiyan.

Maganin ciwon Mara bayan saduwa na asibiti akwai Wanda ake cewa ibuprofen, zaki iya shiga kowane kyamis ki tambaya, idan babu sai ki ce a baki naproxen sodium, shima yana maganin ciwon mara bayan saduwa, shima idan babu sai ki tambayi acetaminophen, shima yana maganin ciwon mara bayan saduwa.

Bayan maganin asibiti, dabarun maganin ciwon mara bayan saduwa akwai samun tsumma me kyau a rika sakawa a ruwan dumi Ana dorawa daidai marar.

Karanta Wannan  Ciwon mara bayan saduwa

Hakanan ana iya yin wanka da ruwan dumi dan samun sauki daga ciwon mara bayan saduwa.

Hakanan ana iya kwanciya a huta bayan jima’i, hakan ma na sanya a samu sauki insha Allah.

Daya daga cikin abubuwan dake kawo ciwon mara bayan jima’i shine idan mace na fama da bushewar gaba.

Dan haka idan kin san kina fama da matsalar bushewar gaba, sai ki yi amfani da mai irin su man zaitun, man kwa-kwa ko a siyo na asibiti dan shafawa a madadin ruwan gaba.

Idan kin san kina fama da ciwon mara bayan saduwa, sai ki daina yin goho ko kwaciya mijinki na hawa samanki kuna juma’i, saboda hakan nasa mazakutarsa ta rika shiga cikin farjinki sosai wanda zai kawo miki ciwon mara bayan gama jima’in.

Karanta Wannan  Ciwon mara na sha'awa

Maimakon yin goho, ko kwanciya mijinki ya hau samanki, sai ki kwanta a gefen dama no gefen hagu mijinki ya kwanta a bayanki ku yi jima’i a haka, ko kuma shi mijinki ya kwanta ki hau kanshi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *