Babban maganin farin jinin samari shine yin Addu’a.
Yin addu’a musamman a karshen dare ki gayawa Allah abinda kike so zai sa ki samu farin jinin samari da yardar Allah.
Abubuwan da zaki tsare sun hada da:
Ki zama me tsafta.
Kamun kai.
Iya magana.
Kar ki zama me rashin kunya.
Iya kwalliya, saidai hakan ba yana nufin nuna tsiraicin ki ba.
Yawanci zaki ga farin jini daga Allah ne, amma babu abinda ya gagari Allah, idan kika dukufa wajan addu’a, zaki samu abinda kike so.