Wednesday, January 15
Shadow

Maganin girman nono na budurwa

Girman nono abu ne da ‘yan mata da yawa ke son samu,saidai a yayin da shekarunki kanana ne ko kuma baki dade da balaga ba, nononuwanki ba lallai su yi irin girman da kike so ba.

Babbar hanyar da ta fi inganci wajan kara girman nono itace hanyar yin tiyata a asibiti.

Bayan ita kuma sai ta hanyar motsa jiki. Motsa jiki musamman wanda ya shafi daga hannuwa sama da saukesu, yana taimakawa wajan kara girman nonon mace.

Bayan nan kuma, masana sun bada shawarar a rika zubawa nono ruwan sanyi, ko da kin yi wanka da ruwan dumi, kina iya zubawa nononki ruwan sanyi, hakan na sa su mike.

Karanta Wannan  Gyaran nono a sati daya

Hakanan bayan Nono ya fara girma,masana sun bada shawarar a rika saka rigar mama wadda zata dagoshi sama, idan rigar mamanki ta fara saki, sai ki canja wata.

Masana sun bada shawarar a daina shan taba.

A kiyaye kada a yi kiba sosai.

A wani kaulin, Man Aloe Vera na taimakawa sosai wajan kara girman nono.

Hakanan man zaitun shima wasu bayanai sunce yana taimakawa wajan kara girman nono idan ana shafashi akan nonon.

A wani kaulin kuma ana hada gurji, kukumba, da kwai a kwaba a rika shafawa akan nono sau daya a sati.

1 Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *