Fuskar mutum na iya yin kaikayi saboda dalilai daban-daban. Zai iya zama saboda bushewa, cizon wani kwaro ko wata rashin lafiyar fata.
Maganin kaikayin fuskar ya danganta ne ga irin dalilin da yasa take kaikayin.
Idan ya zamana lokacin sanyi ne ko kuma ka dade a waje yasa fuskarka ta bushe, to hanya mafi sauki shine a shafa mai.
Hakanan mutanen da suka manyanta, suma fuskarsu na daukar kaikayi saboda yawan shekaru, suma dai masana kiwon lafiya sun ce shafa mai shine mafita.
Bayan wannan kuma akwai wanda ake samun kaikayin fuska saboda cizon wani kwaro kamar sauro da sauransu.
Irin wannan ana barinshi ya warke da kanshi, idan kuma bai warke da kanshi ba to ana iya amfani da soso da sabulu a wanke fuskar.
Ana kuma iya dora ruwan sanyi ko a samu kankara a nade a fuska a dora a wajan.
Ana kuma iya samun maganin rage radadi a sha.
Akwai wanda zaka kuma shi wata cutace data sameshi tasa fuskar tasa ke kaikai.
Irin wannan ya kamata a nemi likitan fatane ya bashi magani.
Shan magani wanda bai amshi mutum ba na iya kawo kaikayin fuska.
A irin wannan yanayi sai a daina shan maganin, ko kuma idan ba za’a iya daina shan maganin ba sai a tattauna batun da likita.
Mutum yana iya cin wani abinci da zai iya kawo masa kaikayin fuska, a irin wannan yanayi, a daina cin abincin sannan a sami mai a shafa a fuskar.