Idan kina son karin Sha’awa ga wasu shawarwari da masana ilimin kimiyyar lafiyar jima’i suka bada shawarar ayi.
Motsa Jiki: Motsa jiki na da matukar muhimmanci ga maza da mata dake son sha’awarsu ta karu. Ba sai an yi gudu ko motsa jiki me wahala ba,ko da kuwa tafiyace ta Akalla mintuna 30 zuwa wata 1 ta isa duk rana. Amma ana son a rika tafiyar da sauri-sauri.
A rage shiga damuwa: Yawan saka kai a damuwa yana matukar kashe kaifin sha’awa. Duk abinda zai saka mutum a damuwa ya guje masa.
A rika samun isashshen Bacci: Samun Isashshen Bacci na da matukar tasiri wajan kara sha’awa. Mace ta tabbatar tana samun baccin akalla awa 6 zuwa 7.
Idan an zo jima’i kada kawai a fara, a rika wasa da juna sosai ta yanda musamman gaban mace zai kawo ruwa dan a ji dadin jima’in.
A rika yin cima me kyau hadi da kayan itatuwa. Cin kayan ciki,kifi, dodon kodi, madara, kankaka,ayaba, da sauransu na taimakawa karin karfin sha’awa.
A rika magana da me gida ana gaya masa irin yanda akw sonsa sannan a rika gayawa me gida irin abinda ake so yayi musamman lokacin jima’i.