Babban maganin kowace irin cuta shine Qur’ani.
Kamar yadda Allah madaukakin sarki ya fada cewa:
“Kuma mun saukar da qur’ani wanda warakane kuma rahama ne ga masu imani, amma ba zai amfani masu laifi da komai ba sai bata” Al-Isra’ 17:82.
Wannan waraka na nufin ta zahiri da badili.
Kamar yanda ma’aikin Allah, Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallan) yake karanta suratul Falaq da Nasi akansa da iyalansa a yayin da suke fama da rashin Lafiya.
Idan da hakan ba waraka bane, ba zai rika yi ba.
Muslim (2192) ya ruwaito cewa, Matar Manzon Allah(Sallallahu Alaihi Wasallam) A’isha ta ruwaito cewa, idan Annabi Muhammad( Sallallahu Alaihi Wasallam) bashi da lafiya, takan karanta masa Falaqi da Nasi ta shafa masa.
Hakanan Muslim (2192) ya ruwaito cewa, Matar manzon Allah(SAW) A’isha tace idan ma’aiki(SAW) daya daga cikin iyalansa basu da lafiya, yakan karanta Falaki da Nasi ya hura da shafa musu a jiki.
Hakanan tace a lokacin da ma’aiki(SAW) yake ciwon ajali, ta rika karanta Falaqi da Nasi tana shafa masa a jiki, tace amma tana amfani da hannuwansa masu albarka.
Dan haka, maganar malamai itace, Qur’ani warakane ga kowace irin cuta ta zahiri ko ta badili, kuma ba’a ware wani bangare na Qur’anin ba, dukkanshine.