Monday, December 16
Shadow

Maganin matsi ciki da waje

Akwai magungunan matsi kala-kala na mata, wasu ana yi dan maganin sanyi, wasu kuma dan gaban mace ya matse.

Idan maganin matsewar gaba ne watau Farji, Akwai hanyar gargajiya da ake amfani da ita.

Wannan hanya itace ta amfani da ruwan sanyi, musamman kamin a sadu da me gida.

Ana zama a cikin ruwan sanyi ne na dan lokaci kamin saduwa, hakan wata hanyar al’adace da ake magance matsalar budewar gaba.

Akwai kuma hanyar matsi da Karo wadda itama ta gargajiyace amma a likitance bata ingabta ba.

Ana kuma yin matsi da kanunfari wanda shima hanya ce ta gargajiya wadda a likitance bata inganta ba.

Karanta Wannan  Amfanin tafasa

Ana kuma yin matsi da Tafarnuwa, ita tafarnuwa an tabbatar tana maganin sanyi amma itama masana ilimin kiwon lafiya sun yi gargadin kada a sakata a cikin farji.

Hakanan ana yin matsi da Yegot, amma wanda bashi da zaki. Ana turashi da yatsa cikin farji ko gindi wanda hakan yana maganin ciwon sanyi.

Hakanan ana hada Yegot din da zuma a tura a cikin gaban mace da yatsa shima yana maganin kaikayin gaba da maganin sanyi.

Hakanan wasu na amfani da alum a gabansu, saidai shima wannan ba’a tabbatar da sahihancinsa ba.

Hakanan akwai masu yin matsi da bagaruwa, saidai shima wannan ba’a tabbatar da ingancinsa ba.

Karanta Wannan  Maganin cizon sauro

Akwai kuma matsi da ake yi da Aloe Vera wanda shi tabbatas in Allah ya yarda yana maganin kaikayin gaba da sanyi.

Akwai kuma masu yin matsi da gishiri,saidai shima wannan al’adace, likitoci sun yi gargadi a kan hakan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *