Wednesday, January 15
Shadow

Maganin rashin sha’awa ga mace

Rashin sha’awa ko raguwar karfin sha’awa ga mata abune dake faruwa yau da gobe kuma yana faruwa da kowace mace a iya tsawon rayuwarta.

A wani lokacin zaki ji karfin sha’awarki ya ragu na dan lokaci ko na kwanaki kadan, a wani lokacin kuma zai iya daukar kwanaki da yawa ko ma watanni.

Kowane mutum da irin karfin sha’awarsa, wani zai ji yana son yin jima’i kullun wani sai bayan satuka ko bayan watanni kai wata ma a shekara ba zata so yin jima’i sosai ba, kowa da kalar karfin sha’awarshi.

Yanayin karfin sha’awarki ba zai taba iya zama a matsayi guda ba a kowane lokaci, ma’ana zai rika yin sama yana kasa, kuma hakan ba matsala bane.

Saidai idan rashin sha’awarki yayi yawa kuma ya fara damunki, to ya kamata a tuntubi likita ko a nemi magani.

Sannan kuma a sani, mafi yawanci ana gadon irin sha’awar iyayene, idan iyayenki na da karfin sha’awa to ke ma zaki iyayin karfin sha’awa, hakanan idan basu da karfin sha’awa, ke ma ba lallai ki yi karfin sha’awa ba.

Karanta Wannan  Alamomin mutuwar azzakari

Abubuwan dake kawo rashin sha’awa ga mace

Wadannan abubuwan da zamu bayyana a kasa suna kawo rashin sha’awa ko raguwar sha’awa ga mata:

Ciki da haihuwa da Shayarwa: A yayin da mace ta dauki ciki, halittar jikinta zata rika canjawa, hakanan a yayin da ta haihu ma da lokacin shayarwa duk zata fuskanci irin wannan canje-canje na halitta Wanda sukan iya kawo raguwar karfin sha’awa ga wasu Matan.

Shan maganin hana daukar ciki: Amfani da hanyoyin hana daukar ciki na iya sanyawa karfin sha’awar mace ya ragu.

Yawan Wahala ko aikin Karfin: Mace me aikin Wahala da yawa ko aikin karfin da ya wuce kima zata iya fuskantar raguwar karfin sha’awa.

Rashin Motsa jiki: Hakanan macen da ko da yaushe take zaune waje data bata son motsa jiki, itama karfin sha’awarta zai iya raguwa, Dan haka ba’a son mace ta yi aikin motsa jiki da yawa hakanan ba’a son ta zauna bata motsa jiki kwata-kwata.

Karanta Wannan  Kaikayin Azzakari

Damuwa da Rashin Kwanciyar Hankali: Idan damuwa tawa mace yawa, tana iya rage mata karfin sha’awa, Dan haka a rage tunani da shiga damuwa da yawa.

Rashin Shiri da masoyi ko miji: Idan ya zamana baki shiri da mijinki ko Baku zaman lafiya, hakan yana taba karfin sha’awarki inda zata iya Ragusa.

Macen da shekarunta suka jaa, ta daina haihuwa, musamman daga shekara 45 zuwa sama, zata iya fuskantar raguwar karfin sha’awa.

Macen dake fama da cutar Infection wadda ake dauka a bandaki Mara tsafta ko wajan jima’i da wadda ke fama da cutar yoyon fitsari duk zasu iya fuskantar raguwar karfin sha’awa.

Shan Magunguna: Akwai magungunan da idan kika fara shansu zasu iya rage mini karfin sha’awa, idan kika lura wani magani da kike sha yasa karfin sha’awarki ta ragu to saiki daina shansa ki nemi madadinsa ko a yi magana da likita ya bayar da madadinsa.

Karanta Wannan  Abubuwan dake tayarwa maza sha awa

Jin zafi lokacin Jima’i: Idan ya zamana mace na jin zafi lokacin jima’i ko kuma bata jin dadin yin jima’in ma’ana bata gamsuwa, ta kawo ruwa ko ta yi inzali to zai zamana ta tsani yin jima’i wanda hakan zai rage mata karfin sha’awa.

Dadewa da Miji ko abokin ma’amala: Yayin da miji da mata suka Dade tare, masana kiwon lafiyar jima’i since karfin sha’awarsu zai iya raguwa, hakan yafi tasiri a bangaren mata, musamman idan ya zamana soyayyar ta ragu saboda ita mace tana jin dadin jima’i ne idan ta yi da Wanda take so ba kamar namiji dake jin dadin yin jima’i da mace ba ko da baya sonta, idan aka kai wannan matsayi saidai kawai a yi zaman hakuri da juna.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *