Idan ana son yin maganin warin baki ga hanyoyin da masana kiwon lafiyar baki suka bayar da shawarar ya kamata a bi dan samun nasara.
A rika wanke baki da goge harshe duk bayan an kammala cin abinci, akwai abin goge harshe na musamman da ake sayarwa, kuma da yawa burushin goge baki ana yinsa ta yanda mutum zai iya amfani dashi wajan goge harshe amma mutane da yawa basu sani ba.
Ka duba bayan burushin goge bakinka, idan kaga yana da kurzuni-kurzuni ko kaushi to alamace zaka iya juya bayan ka goge harshenka dashi duk bayan kammala cin abinci.
Hakanan masana kiwon lafiyar baki da hakora sun bada shawarar rika yin sakace ana cire abinci da ya makale a tsakanin hakora duk bayan kammala cin abinci dan kawar da warin baki.
Hakanan ana son mutum ya rika canja burushin wanke baki akai-akai dan hana warin baki.
Kaucewa cin Albasa da Tafarnuwa shima zai taimaka
Saidai masana sun ce mutane da yawa dake tunanin suna da warin baki basu da warin bakin.
Hanya daya da zaka gane kana da warin baki itace ka tambayi wani na kusa da kai wanda kasan zai gaya maka gaskiya.
Maganin Warin Baki daga ciki:
Warin baki daga ciki mafi yawanci yana samo Asaline idan mutum ya dade bai ci abinci ba.
Karamin misali shine, ka tuna da azumi zaka ji bakinka ko na mutane yana wari.
Dan haka mutum ya daina dadewa da yunwa a rika cin abinci a lokacin da ya dace.
Hakanan rashin tsafta yana sa warin baki.
.aganin Warin baki a masallaci
Dan maganin warin baki, a rika wanke hakora akalla sau biyu a rana, safe da yamma, idan kuma mutum zai iya, ya rika wankewa duk bayan cin abinci.
Sannan a rika goge harshe dan shima abinci na makalewa akansa ya rika wari, mutum kuma ya rika sakacen hakoransa, dan abinci da yawa na makalewa a tsakanin hakora ya rube ya rika wari.
Hakanan ruwan Abarba, na maganin warin baki, kuma kamata yayi a hada ruwan a gida, watau a matseta a gida ko kuma mutum bayan kammala cin abinci sai ya ci abarbar, kada a manta a kuskure baki bayan cin abarbar.
A rika shan ruwa, bushewar baki na daya daga cikin abinda ke kawo warin baki, dalili ma kenan yasa idan aka tashi da safe ake jin warin baki yafi yawa, dan hakane mutum ya rika shan ruwa akai-akai a rana, akalla sau 8 dan kaucewa warin baki.
Hakanan cin Tuffa ko Apple na daya daga cikin abinda ke kawar da warin baki, musamman idan mutum ya ci Albasa ko Tafarnuwa, idan yaci Apple, zai kawar da wannan wari.
Lemu na daya daga cikin abubuwan dake kawar da warin baki, idan mutum na son maganin warin bakinsa, sai ya samu lemun fata ya rika sha.
Shan madara ma na kawar da warin baki sosai. Musamman idan mutum ya ci abinci me sa warin baki irin su Tafarnuwa, Albasa da sauransu, mutum ya sha madarar ruwa, zai samu saukin warin bakin.
Shan Yegot, bincike ya tabbatar da cewa, Shan Yegot yana kawar da warin baki shima. Dan samun sakamako me kyau, mutum ya rika shan Yegot akalla sau daya a rana dan kawar da warin baki.