Friday, December 12
Shadow

Magidanci ya sayar da Dansa me watanni 11 kacal a Duniya ya buga caca da kudin

Wani magidanci ya sayar da dansa me watanni 11 kacal a Duniya inda yayi amfani da kudin wajan buga caca.

Ya sayar da dan nasu ne ba tare da sanin matarsa ba.

Lamarin ya farune a yankin Tangerang, West Jakarta na kasar Indonesia.

Matarsa ta koma gida bata ga dan nasu ba inda ta tambayeshi, da ya fara mata kame-kame amma daga baya ya fito ya gaya mata gaskiya.

Tuni ‘yansandan ‘yankin su suka kamashi.

Ya dai sayar da danne akan farashin £730 kuma tuni suma wanda suka sayi dan aka kamasu.

Karanta Wannan  Wata Mata Ta Cika Da Mamaki Bayan Da Ta Je Duba Gidan Da Ta Ke Ginawa Ta Tarar Wasu Sun Tare A Gidan

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *