
A lokacin bikin Tauraron Kannywood, Jamilu Kochila, da yawa sun yi alkawarin bashi gudummawa amma basu cika Alkawari ba.
Daga cikin cikin wadanda suka yi wannan alkawarin, akwai dan Kasuwa, Baballe Na’abba wanda yayi Alkawarin bayar da gudummawar Naira Miliyan 10.
Saidai daga baya a yanzu yace zai baiwa Amarya da Ango kujerun zuwa Makkah da Madina.
Mansurah Isah ce ta bayyana hakan.