Majalisar Wakilan Najeriya ta bukaci ministan sufurin kasar ya gurfana a gabanta domin amsa tamboyoyi kan matsalolin da ake ci gaba da fuskanta a kan hanyar jirgin kasa na Abuja zuwa Kaduna a ‘yan kwanakin nan.
Ko a makon da ya gabata jirgin kasan da ya taso daga Abuja zuwa Kaduna ya goce daga hanya, matakin da ya bar fasinjoji cikin zullumi.
Kan haka ne Majalisar ta amince da matakin gudanar da bincike domin fahimtar matsalar da kuma shawo kanta.
Ɗan majaisa Umar Ajilo mai wakiltar Makarfi da Kudan ya ce ya gabatar da ƙudirin ne na gaggawa domin duba lamarin.
“Ni ɗan Kaduna ne kuma duk lokacin da na hau jirgin tare da mutane zan ji suna nuna fargaba,” in ji.