Friday, December 19
Shadow

Man Fetur din Najeriya yayi kwantai a kasuwar Duniya

Rahotanni sun ce ganga kusan miliyan 20 na danyen man fetur din Najeriya da ake son sayarwa a tsakanin watannin Disamba zuwa January har yanzu yana nan ba’a sayar dashi ba.

Kafar Reuters tace itama kasar Angola danyen man nata nacan Jibge an kasa sayar dashi.

Rahoton yace kasashen biyu na ta kokarin ganin sun samu masu sayen danyen man fetur din nasu amma abu ya faskara.

Rahotanni sun ce kasar China wadda tana daya daga cikin manyan masu sayen danyen man na kasashen Afrika ta fara komawa sayen man daga kasashen Larabawa saboda yafi saukin farashi da kuma saukin sufuri.

Karanta Wannan  Karanta Jadawalin wanda suka halarci taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar PDP

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *