Wednesday, January 15
Shadow

MASANA’ANTAR KANNYWOOD WAJE NE NA GYARA TARBIYYA BA GURƁATA WA BA, CEWAR MARYAM SANI

Wata sabuwar Jaruma a masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Maryam Muhammad Sani ta bayyana Kannywood ɗin a matsayin wata masana’anta wacce ake faɗakarwa da gyaran tarbiyyar al’umma ba wai ɓata tarbiyya ba.

Maryam ta bayyana haka ne ta cikin wata tattaunawarta da Jaridar Dokin Ƙarfe TV inda ta ƙara da cewa “Na shigo masana’antar Kannywood ne domin ina da gudunmawar da zan bayar game da gyaran tarbiyyar al’ummar nan tamu”. In jita.

Maryam ta kuma ƙara da cewa “Bai kamata mutane suna ƙyamatar ƴan fim ba. Domin fim harka ce ta kawo cigaba da magance matsalar tsaro da raya al’adun Hausa Fulani”. A cewar ta.

Daga ƙarshe Malama Maryam ta kuma ƙara da cewa tarbiyya tana farawa ne tun daga gida, dan haka masana’antar Kannywood waje ne na koya tarbiyya ba ɓatawa ba”. In ji ta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *