Sanata Ali Ndume ya bayyana cewa,Masu baiwa shugaban kasa,Bola Ahmad Tinubu shawara ne ke saka mutane a Wahala.
Sanata Ndume ya baiwa shugaban kasar shawarar ya daina biyewa irin wadannan mutane dake son hadashi fada da ‘yan Najeriya.
Sanatan ya bayyana hakane a wata sanarwa da ya fitar a Abuja.
Ya kara da cewa, Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu yana da kyakkawan fatan farantawa ‘yan Najeriya rai amma masu bashi shawara ne matsalar.
Yayi fatan cewa idan shugaban kasar ya dawo gida Najeriya zai duba wannan matsala ta tsadar rayuwa.
Yace mutane basu da wadatar da zasu iya rayuwar wahalar da ake kakaba musu.