Tuesday, March 17
Shadow

Masu ikirarin Jìhàdì sun kàshè manoma da masunta 40 a jihar Borno

Rahotanni sun bayyana cewa ƙungiyar mayaƙan ÌŚWÀP ta kashe wasu manoma 23 da kuma masunta a wani hari da ta kai ƙauyen Malam Karanti kusa da Baga a karamar hukumar Kukawa na jihar Borno.

Majiyoyi sun ce mayaƙan sun tara manoman da kuma masunta ne wuri ɗaya, inda suka kashe manoman wake 23.

An hana mazauna garin ɗaukar gawawwakin ƴan uwansu da aka kashe, kamar yadda gidan talabijin na Channels a Najeriya ya ruwaito.

“Mun yi ƙoƙarin zuwa don ɗaukar gawawwakin waɗanda aka kashe tare da jami’an tsaro, sai dai mayaƙan sun hana mu yin haka. Iyalai da dama na jiran gawawwakin ƴan uwansu,” in ji wani ɗan garin.

Karanta Wannan  Wata Sabuwa: Kalli Abinda Dan Damben Najeriya, Anthony Joshua yayi bayan Khàdàrìn daya rutsa dashi da abokansa biyu inda abokan suka rasu da ya sa aka fara zarginsa

Ƙauyen Malam Karanti matattara ne na mayaƙan ISWAP, wuri kuma da fararen hula ke noma da kamun kifi duk da irin barazanar da suke fuskanta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *