
Wannan hanyar Bida ne jihar Naija
Inda aka samu tsaikon ababen hawa wanda aka fi sani da Go Slow.
Saidai wasu motocin gwamnati sun zo wucewa bisa rakiya jami’an tsaro sojoji da ‘yansanda
Sun bi one way, watau hanya daya dan su samu su wuce sojoji na buda musu.
Ko da masu manyan motoci suka ga haka, sai suka kicciya motocinsu akan hanyar suka hana kowa wucewa.
Sun ce indai ba za’a gyara hanyar kowa ya wuce ba to babu wanda zai wuce