
Mambobin kungiyar All Progressives Congress Young Leaders Alliance (APC-YLA) a ranar Juma’a sun gudanar da zanga-zanga a gaban hedikwatar Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) da ke Abuja.
Sun bukaci hukumar da ta gaggauta dawo da binciken zargin cin hanci da rashawa da ake yi wa Bello Matawalle, wanda yanzu haka shi ne karamin ministan tsaro.
Kungiyar, wadda ta bayyana kanta a matsayin wata kungiya mai matsin lamba ta siyasa dake da tushe a Kaduna, ta zargi EFCC da yin shiru game da wannan batu duk da korafe-korafen da dama da kuma alkawarin da ta riga ta dauka na gudanar da bincike a kan tsohon gwamnan jihar Zamfara.
A wata takarda da suka mika yayin zanga-zangar, kungiyar ta tambayi dalilin da yasa EFCC ta kasa daukar mataki a kan Matawalle duk da zarge-zargen aikata ba daidai ba na kudi daga shekarar 2019 zuwa 2023.
Yayin da yake magana da manema labarai, Mohammed Ireyi, mai magana da yawun APC-YLA, ya ce yadda EFCC ke yin shiru a kan wannan lamari na saka mutane cikin shakku kan gaskiyar ayyukanta.