
Matashiya daga jihar Benue, Terzungwe Juliana Iorzaa me shekaru 28 ta samu aikin tuka motar dakon man fetur ta Dangote.
Ta kammala karatu daga jami’ar Akperan Orshi College of Agriculture Yandev, Juliana.

Sannan dama can tana da kwarewa a iya tuka babbar motar dakon mai, a yanzu dai Dangote ya dauke aiki har an bata mota.
