Katafariyar matatar mai mallakar hamshaƙin ɗankasuwan nan, Alhaji Aliko Dangote ta ɗage ranar da zata fara fitar da man fetur domin sayarwa a cikin ƙasar zuwa watan Yuli.
Attajirin ya ce an ɗage ne saboda sun samu wani jinkiri, amma ya bayar da tabbacin fara samar da man fetur ɗin a tsakiya zuwa ƙarshen watan goben, kamar yadda kafar watsa labarai ta Channels TV ta bayyana.
Tuni dai wasu dillalan man suka yi rajista da kamfanin domin fara ɗaukar man tare da rarraba shi a fadin ƙasar.
Haka kuma kamfanin ya fara sayar da man dizil da na jirgin sama a ƙasar.
Tun a watan Disambar 2023 ne matatar ta fara aiki, inda ta ke tace gangan danyen mai 530,000 a rana.
Mahukunta a ƙasar na fatan fara samar da man fetur daga matatar ta Dangote za ta taimaka wajen kawo ƙarshen matsalar ƙarancin mai tare da rage tsadarsa a ƙasar.
Najeriya ita ce ƙasar da ta fi kowacce arzikin ɗanyen mai a nahiyar Afrika, sai dai ta dogara ne da shigo da tataccen mai daga waje saboda rashin matatun da za su tace a cikin gida.