
Matatar man fetur din Dangote ta rage farashin man fetur dnta inda a yanzu take sayar dashi akan Naira 840 maimakon 880 da yake a baya.
Hakan na wakiltar ragin kaso 4.5.
Bincike ya bayyana cewa Dangote ya rage farashin nasa ne bayan da farashin danyen man fetur ya fadi a kasuwar Duniya zuwa dala $67.50 daga Dala sama da $70 da yake a baya.
Wasu sauran kamfanonin ma sun rage farashin man fetur din nasu kamar yanda Dangote yayi.