
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, amfanin tsarin tsaron da ake kanshi a yanzu, ya kare.
Ya bayyana cewa, samar da ‘yansandan jihohi yanzu ba magana bace kawai ta fatar baki ba, abune da ya zama dole dan samarwa ‘yan kasa tsaro.
Shugaban yace jami’an tsaron da ake dasu yanzu wanda gwamnatin tarayya ke kula dasu aiki ya musu yawa kuma basa iya samar da tsaron yanda ya kamata
Shugaban yace, dolene a baiwa jihohi dama su samar da ‘yansandan jihohi da zasu ira aiki dan kare garuruwa da unguwanni, yace hakan ko yi ne ga tsarin tsaro da ake dashi a kasashen da suka ci gaba.
Shugaban ya bayyana hakane a wajan taron tataunawa kan canja fasalin kudin tsarin mulkin Najeriya da kuma canja fasalin harkar tsaro wanda aka gudanar a Abuja ranar Litinin wanda kwamitin kula da canja kundin tsarin mulkin Najeriya na majalisar tarayya ya shirya.
Shugaban ya kara da cewa dolene a canja fasalin kundin tsarin mulkin ta yanda zai samarwa ‘yan Najeriya tsaro yanda ya kamata.