
Shahararren mawakin Najeriya, Davido ya bayyana cewa ya tafka asarar Naira Miliyan 495 saboda cacar da ya buga akan cewa Najeriya ce zata ci Morocco.
Davido dai wanda yayi suna wajan yin caca da son kwallo, ya saka cewa, Najeriya ce zata ci amma sai Morocco ta yi nasara.
Davido ya wallafa rasit din cacar da yayi a shafinsa na sada zumunta.