
Bayan tsawon lokaci ba a ji ta bakinsa ba dangane da faruwar al’amuran siyasa, tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Ebele Jonathan ya ɓara inda ya yi gargaɗin cewa “abu ne mai haɗari ɗora Najeriya a kan turbar jam’iyya guda ɗaya”.
Ba kasafai dai ake jin bakin Goodluck Jonathan ba a al’amura kasancewarsa mutum mai kawaici da rashin son yawan magana.
To sai dai a ranar Larabar nan, tsohon shugaban na Najeriya yayin wata lacca da aka shirya a Abuja domin tuna wa da marigayi Edwin Clerk, dattijo ɗan ƙabilar Ijaw wanda ya rasu yana da shekara 97, Jonathan ya ja hankalin gwamnati da jam’iyya mai mulki ta APC da ake zargi da mayar da ƙasar ƙarƙashin tsarin jam’iyya guda.
Kalaman Goodluck Jonathan
Tsohon shugaba Goodluck Jonathan ya ce duk wnai yunƙurin mayar da Najeriya kan tsarin jam’iyya guda ɗaya ta hanyar makircin siyasa domin dacewa da buƙatun wasu ka iya zama haɗari ga ƙasar.
“Idan har dole, a matsayinmu na ƙasa, sai mun runguni tsarin jam’iyya ɗaya tal, to dole ne a ƙwararru su tsara kan – kuma ya zama dole mu san cewa za mu yi hakan.”
“Amma idan muka cimma tsarin ta bayan gida ta hanyar maguɗi, to fa za mu shiga cikin ruɗu.”In ji Goodluck.
Duk da mista Jonathan ya amince cewa wasu ƙasashen sun dabbaƙa tsarin na jam’iyya ɗaya tilo kuma suka yi nasara, amma ya ce ƙasashen da suka samu nasarar sun kasance masu tarihi da yanayin al’adu guda ɗaya, inda ya yi gargaɗin cewa Najeriya ƙasa ce mai sarƙaƙiyar addini da al’ada da siyasa saboda haka tana buƙatar tsarin da zai tafi da kowa.
“E, ƙasashen da ke tafiya kan tsarin jam’iyya ɗaya, sun samu nasara. Kwarai, tsarin ba zai zama abun ƙyama ba saboda Julius Nyerere na Tanzania ya yi tsarin domin tabbatar da ƙasar ta kasance cikin zaman lafiya a farkon shekarun samun ƴancin kai.”
“..Amma ƙasa kamar Najeriya mai kabilu da harsuna da addinai – Kiristanci da Musulunci, …Idan muka bar jam’iyyu masu yawa, wasu ka iya na addini ko ƙabilanci to ka ga haɗin kai zai zama abu mai wuya. Amma an tsara abin yadda ya dace; ba haka nan ya faru ba” In ji Goodluck Jonathan.
“Da wuya a mayar da Najeriya mai bin jam’iyya ɗaya”
Malam Kabiru Sufi, malami a kwalejin share fagen jami’a ya ce duk da irin wawason da jam’iyya mai mulki ta APC ke yi a yanzu haka ba ya nuna cewa jam’iyyar ka iya zama jam’iyya ɗaya tilo a Najeriya.
“Duba da cewa har yanzu ana jin motsin sauran jam’iyyun na hamayya da ma ƙoƙarin haɗa da masu hamayyar ke yi na nuna cewa ba a ɗauki hanyar komawa tsarin jam’iyya ɗaya a ƙasar ba.
Har yanzu jam’iyyar APC ba ta yi shekarun da jam’iyyar PDP mai hamayya ta yi a baya ba tana mulki. PDP ta kwashe shekaru 16 kuma ƴan jam’iyyar sun ta yin iƙrarin cewa ba za su bar wata jam’iyya ta yi mulki ba. Amma bayan haɗaka da abokan hamayya suka yi daga ko’ina sai ga shi sun kayar da ita. To ita ma APC hakan ka iya faruwa a kanta.” In ji Malam Kabiru Sufi.
To sai dai Farfesa Abubakar Kari masanin kimiyyar siyasa kuma malami a Jami’ar Abuja ya ce nan gaba idan ba a yi taka tsan-tsan ba Najeriya za ta iya komawa ƙasa mai jam’iyya ɗaya.
“Wannan gagarumin koma-baya ne ga ga ɓangaren adawa, kuma koma-baya ne ga tsarin dimokuraɗiyya saboda hakan na ƙara wa jam’iyya mai mulki ƙarfi, kuma dimokraɗiyya ba ta ƙarko sai da jam’iyyun adawa masu ƙarfi,” in ji Farfesa Kari.
Farfesa Kari ya ce illar mamaye masu hamayya da mayar da su ƙarƙashin jam’iyya mai mulki ita ce “za a kai yanayin da gwamnati mai mulki za ta rinƙa gudanar da duk abubuwan da take son yi ba tare da masu hamayya sun taka mata burki ba.”
Shi ma tsohon gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa , ya ce a yanzu babu wata hamayya da ta rage a fagen siyasar Najeriya.
A tattaunawarsa da BBC ya ce ‘yan siyasar ƙasar su ne ke hamayya da kansu da cutar juna game da neman muƙamai ba tare da sun anfana wa talakawa wani abu ba.
Tsohon gwamnan ya yi zargin cewa duk wannan sauya sheƙa da ‘yan siyasar na ɓangaren hamayya ke yi suna tafiya jam’iyya mai mulki ba don su amfanin talaka suke yi ba, face don kansu suke yi, saboda haka ya ce siyasar hamayya ta matu a ƙasar a yanzu – babu aƙida.