Babban Fasto na cocin Daystar Christian Centre Sam Adeyemi ya bayyana cewa, maza su daina damun kansu da son kara girman mazakutarsu.
Ya bayyana hakane a wajan zaman cocin na ranar Lahadi.
Yace mafi yawan ci matsi ne musamman daga kafafen sadarwa zamani ke sanya mutane neman maganin karin girman mazakuta wanda daga baya da yawa ke yin danasanin yin hakan.
Yace iya amfani da mazakutar wajan gamasar da macene shine abu mafi muhimmanci ba girmanta ko tsawonta ba.
Yace maza su mayar da hankali wajan fahimtar abinda matansu ke bukata a gado yafi neman maganin kara girman mazakuta amfani.