Wednesday, January 15
Shadow

Me ake nufi da aure

Aure wata tarayya ce ko zama tsakanin namiji da mace wadda Addini da Al’ada sun mince dashi.

Ana aure ne tsakanin Namiji da mace wanda suka amince su zauna tare su gina iyali da samun zuri’a.

A musulunci, Aure sunnar Annabi Muhammad(Sallallahu Alaihi Wasallam) ne.

Hanyar aure itace mafi tsafta ta samun zuri’a da cikar mutunci da nasaba.

Duk wanda aka sameshi ta hanyar aure to zaka ga murna ake dashi, ba’a tsangwamarshi ba’a yi masa gori, saboda yana da uwa da uba.

Shi kuwa wanda aka samu ba ta hanyar aure ba, duk da ba laifin shi bane zaka ji ana ce masa shege da gorin Uba da sauransu.

Karanta Wannan  Addu ar saduwa da iyali

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *