Yawancin abinda ke kawo ruwan nono shine haihuwa.
Bayan mace ta haihu, ruwan nononta na zuwa sosai.
Bayan haihuwa akwai wasu abubuwan na daban da kan iya kawowa budurwa ruwan nono:
Yawan tabawa da matsa nonon budurwa yana iya sawa ya kawo ruwa.
Shan wani magani da jikin budurwar be yi amanna dashi ba yana iya sata reaction ruwan nononta ya kawo.
A wasu lokutan ma haka kawai babu dalili, nonon budurwa zai iya kawo ruwa.
Yanda ake tsayar da zubar ruwan nono
Zubar nono na raguwa da kanta daga lokaci zuwa lokaci.
Amma akwai abubuwan da za’a iyayi dan magance matsalar.
A daina matsa nonon.
Wasu lokutan ana gwada daure nonon da tsumma me kyau.