Wednesday, January 15
Shadow

Mining din Major sun fitar da sanarwa ta musamman

Shahararren Mining din $Major na Telegram sun fitar da sanarwa yayin da masu yinsa suke tsammanin jin ranar shiga kasuwa.

A baya dai $Major sun sanar da cewa a watan October zasu fitar da ranar da zasu shiga kasuwa, a yayin da ake tsammanin wancan bayani, sai ga Major din sun sanar da cewa, nan da ranar 11 ga watan October da muke ciki ne zasu daina bayar da damar sayen Major da kudi.

Duk da yake ba wannan bayanine ‘yan baiwa suke bukatar ji ba, amma wannan alamace dake nuna cewa, $Major din suna shirin shiga kasuwa.

A cikin jawabin da suka fitar a yau, Major sun ce sun tunkari hanyar Listing watau shiga kasuwa amma har yanzu mutum zai iya ci gaba da tara point dinsu.

Karanta Wannan  Menene crypto da Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *