
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya amince da murabus ɗin ministan kimiyya da fasaha na Najeriya Geoffrey Uche Nnaji.
A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Najeriya Bayo Onanuga ya fitar, ya ce shugaban ya amince da murabus ɗin ministan, wanda ya biyo bayan zarginsa da aka yi da amfani da digirin bogi.
An dai zargi tsohon minista ne da amfani da digirin bogi daga Jami’ar Najeriya ta Nsuka, lamarin da ya ja hankalin ƴan ƙasar matuƙa, duk da ya musanta.
Njaji ya ce ana masa bita da ƙulli ne, lamarin da ya zargi “abokan hamayyarsa a siyasa” da yunƙurin ɓata masa suna.
Tinubu ya yi godiya a gare shi “bisa hidimta wa Najariya” sannan ya yi masa fatan alheri.