
Gwamnan jihar Legas, Sonwo Olu ya bayyana goyon bayansa ga zarcewar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a shekarar 2027.
Ya bayyana hakane a yayin da yake jawabi ga ma’aikatan jihar Legas din inda yace yana aiki ne tukuru wajan inganta rayuwar su.
Yace ana ganin alfanun tsare-tsaren gwamnatin Tinubu inda yace misali an samu ci gaba ta fannin noma, farashin kayan abinci ya sauka.