Jika a wajan tsohon shugaban kasa, Alhaji Shehu Shagari, Bello Shagari ya bayyana cewa sun kasa kula da gidan kakansu, tsohon shugaban kasar ne saboda basu saci kudi ba kuma dalilin haka yasa ba zasu iya kula da gidan ba.
Ya bayyana hakane a matsayin martani ga wani dake tambayarsa me yasa suka kasa kula da gidan kakan nasu.
Alhaji Shehu Shagari na daya daga cikin tsaffin shuwagabannin da akewa kallon mutanen kirki saboda basu yi sata ba.