
Tsohon gwamna jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bayyana cewa, gamayyar ‘yan adawa sun amince da shiga jam’iyyar ADC wadda zasu yi amfani da ita wajan kayar da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zabe a shekarar 2027.
El-Rufai ya tabbatar da hakan ne a shafinsa na X sannan ya bayyana cewa, Sun baiwa tsohon ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola mukamin sakataren jam’iyyar na riko.
Aregbesola ya bayyana cewa ya amince da wannan mukami da aka bashi kuma jam’iyyarsu ta jama’ace a lokacin zabe da bayan zabe.