Thursday, May 22
Shadow

Mun fi kowacce ƙungiya ƙoƙari a gasar zakarun turai – Kocin Arsenal

Mun fi kowacce ƙungiya ƙoƙari a gasar zakarun turai – Kocin Arsenal.

Kocin Arsenal Mikel Arteta ya ce ƙungiyar tasa ce ta fi kowacce ƙoƙari a gasar zakarun Turai ta Champions League ta bana duk da kashin da suka sha a hannun Paris St-Germain.

BBC Hausa ta rawaito cewa Arsenal ɗin ta je filin wasa na Parc des Princes ne da zimmar rama ƙwallo ɗaya da aka zira mata a gidanta a wasan farko domin kaiwa wasan ƙarshe na gasar.

Sai dai duk da damarmakin da suka ƙirƙira, ‘yanwasan Arsenal ɗin ba su iya yin nasara ba.

Ƙwallayen da Fabian Ruiz da Achraf Hakimi suka ci ne suka taimaka wa PSG din, inda har sai a minti na 76 Bukayo Saka ya farke wa Arsenal ɗaya, inda wasa ya tashi 3-1 gida da waje.

Karanta Wannan  YANZU-YANZU: Kalli Hotunan yanda Motar rusau ta bayyana a gidan Sarkin Nasarawa, inda Sarki Aminu Ado Bayero yake zaune yanzu haka

“Saura ƙiris, ƙiris ya rage mu sauya sakamakon wasan, amma kuma aka fitar da mu,” a cewar Arteta.

“Ina matuƙar alfahari da ‘yanwasana 100 bisa 100. Ba na jin akwai wata tawaga [da ta fi Arsenal] a gasar bisa abin da na gani, amma dai an cire mu.

“A wannan gasar, akwai da’irar yadi na 18, da masu tsaron raga, da masu cin ƙwallo, kuma nasu ne suka fi ƙoƙari a wasannin biyu.”

Saboda gaza kaiwa wasan ƙarshe a Champions League karon farko tun 2006, kocin na Arsenal ya ce ‘yanwasansa sun yi ta kuka bayan wasan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *